Jam’iyar PRP ta ce kudin Form ga masu sha’awar tsayawa takarar Shugaban Kasa Naira Miliyan 10 ne, sai kuma Gwamna Naira Miliyan 2 da dubu 500.

Haka kuma Jam’iyar ta ce kudin Form din Dan Majalisar Dattawa Naira Miliyan 1 da dubu 500 ne sai kuma Dan Majalisar wakilai dubu 250, da kuma Dan Majalisar Jiha Naira dubu 100.

Shugaban Jam’iyar na Kasa Mista Falali Bello, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja, inda ya ce Naira dubu 500 ga Shugaban Kasa da dubu 200 ga Gwamna a matsayin kudin Form kamar yadda ake yadawa karya ne.

Haka kuma ya ce Jam’iyar ta fitar da sanarwar hakan a ranar 16 ga watan Afrilu tare da ka’idojin ta na sayar da Form din kamar yadda hakan ya ke cikin ka’idojin hukumar INEC ta Kasa.

Alhaji Falalu Bello, ya ce masu bukata ta musamman wanda suke sha’awar tsayawa takara a Jam’iyar Form din su kyauta ne.

Kazalika, ya ce Jam’iyar ta ragewa Mata kaso 50 cikin 100 na kudin Form din domin tsayawa takara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: