Jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), ta yi gargaɗi ga dukkan mambobinta da ke ƙulla shirin shiga sabuwar haɗakar siyasa cewa suna “kallon su sosai” kuma za su ɗauki matakin da ya dace a lokacin da ya dace.
A yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan taron Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar ranar Laraba, Mukaddashin Shugaban jam’iyyar, Ambasada Umar Damagum, ya bayyana cewa mambobin jam’iyyar su sani babu inda ya fi gida dadi.
Ya ƙara da cewa babu wata jam’iyya da za ta iya ba su dama da kulawar da PDP ta ba su tun farko.
Ambasada Damagum ya kuma ja kunnen su cewa soyayya da wasu jam’iyyu ba za ta daɗe ba, inda ya nuna tabbacin cewa da dama daga cikinsu za su dawo gida nan ba da jimawa ba.