Haɗakar hammayar ADC a Najeriya ta tabbatar da naɗin Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Ƙasar, Sanata David Mark a matsayin sabon shugabanta na ƙasa.
Sanata David Mark, ya bayyana cewa ƙawancen ADC, haɗaka ce da ta shafe watanni ana tattaunawa domin samar da ita.
Ya ambato manyan matslolin tsaron da ke addabar jahohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Sokoto da Borno da Yobe da sauran su, da cewa duk wani da ya damu da halin da ake ciki mai alaƙa da hakan, ya amince da shiga wannan haɗaka tasu.
Ya ce duk waɗanda suka hallara a taron da zuciya ɗaya suka amince da dunkikewar.
David Mark ya kuma ce daga cikin fatansu shi ne ceto Najeriya da kuma al’ummar kasar.
A taron haɗakar na jiya ne aka tabbatar da naɗin tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa.