Jam’iyyar APC reshen jihar Jigawa ta sanar da kudurin ta na samar da shugabanninta na jihar ta hanyar sulhu

0 62

Jam’iyyar APC reshen jihar Jigawa ta sanar da kudurin ta na samar da shugabanninta na jihar ta hanyar sulhu.

Shugaban kwamitin zabe wanda aka aiko daga helkwatar jam’iyyar ta kasa, Alhaji Haruna Musa ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai karin haske bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Ya ce an amince da sulhu a zabukan mazabu da na kananan hukumomin da aka gudanar a jihar, inda ya kara da cewa taron na jihar ma zai bi irin wannan hanyar.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana kwarin gwiwarsa na gudanar da babban taron jam’iyyar cikin kwanciyar hankali da nasara a jihar.

Gwamnan wanda mataimakinsa Malam Umar Namadi ya wakilta, ya ce akwai mutunta juna, zaman lafiya da hadin kai tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a jiharnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: