Jam’iyyar APC ta amince cewa manufofin Tinubu sun ƙara jefa ƴan Najeriya cikin mawuyacin hali
Jam’iyyar APC mai mulki ta amince cewa manufofin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya ƙaddamar sun ƙara jefa ƴan Najeriya cikin wahalhalun tattalin arziƙi.
Wannan amincewar ta fito ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar, Barista Felix Morka, ya fitar yayin da yake mayar da martani ga tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa na yankin Arewa maso Yamma, Salihu Mohammed Lukman.
Lukman ya zargi jam’iyyar da rashin kyakkyawan shugabanci, inda ya bayyana cewa tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Ahmed Tinubu na yanzu sun kasa cika alkawurran yaƙin neman zaɓen da suka ɗauka.
Lukman ya kuma yi kira ga shugabannin jam’iyyun adawa su haɗa kai tare dayin aiki tuƙuru don kayar da gwamnatin APC a zaɓen 2027 mai zuwa.
A martaninsa, Barista Morka ya ce Shugaba Tinubu yana ɗaukar matakai masu tsauri don sake fasalin tattalin arzikin ƙasar da ya daɗe yana fama da matsaloli, amma ya amince da cewa waɗannan gyare-gyare sun ƙara jefa ƴan kasar cikin mawuyacin hali.
A kan batun Lukman, Felix Morka ya ce Lukman na neman suna ne a siyasa tun bayan ficewarsa daga matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa.