Jam’iyyar APC ta bayyana cewa bata ji dadin yadda Jega ya kwatanta ta da PDP ba

0 88

Jam’iyyar APC ta mayar da martani kan maganganun baya-bayan nan da aka danganta ga tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega.

Jega ya shawarci ‘yan Najeriya da kada su zabi jam’iyya mai mulki APC da jam’iyyar adawa ta PDP a babban zaben 2023.

Jam’iyyar APC ta bayyana cewa, bata ji dadin yadda Jega ya kwatanta ta da jam’iyyar PDP ba.

A cewar APC, wannan mummunan kwatance ne wanda yake ba daidai ba kuma ba gaskiya bane.

Ta ce a halin yanzu, tana kokarin gyara kura-kuran PDP ne na tsawon shekaru 16 da suka gabata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: