Jamiyyar APC mai mulki a Najeriya ta ce bai kamata tsohon gwamnan jihar Kano kuma ɗan takarar shugabancin ƙasar na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023 Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya riƙa yin kalamai sakaka, ba tare da kame baki da lura da abin da zai iya haifarwa a kan lamarin jihar Kano ba.
Jam’iyyar ta ce a matsayin Kwankwaso na dattijo a ƙasa kamata ya yi ya mayar da hankalinsa kan lalubo duk wata hanya ta siyasa da lumana don magance rikicin masarautar jihar maimakon rura wutar dambarwar.
Kiran na kunshe ne a martanin da jam’iyyar ta APC ta mayar wa da Kwankwason, mai ɗauke da sa hannun Sakataren yaɗa labaranta na ƙasa Felix Morka, kan zargin da tsohon ɗan takarar ya yi cewa gwamnatin APCn, na neman haddasa rigima a jihar ta Kano, domin a kai ga kafa dokar ta-ɓaci ta yadda za ta yi amfani da hakan domin karbe jihar.
A lokacin ƙaddamar da wani aiki da gwamnatin jihar ta yi ne, Sanata Rabi’u Musa Kwankwason ya yi zargin cewa wasu sun hada baki da jagororin jam’iyyar APC suna kokarin fakewa da batun rikicin masarautar Kano su tayar da rikici, don gwamnatin tarayya ta samu damar ƙaƙaba dokar ta ɓaci. Sai dai Fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da zargin da Kwankwason ya yi, tana bayyana shi a matsayin wanda ba shi da tushe.