jam’iyyar APC ta ce za ta gudanar da zaben shugabanninta da babban a taronta na kasa a watan Yuni.

Amma sai shugabannin jam’iyyar sun amince da hakan.

Sakataren kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, James Akpanudoedehe, ne ya bayyana hakan a jiya yayin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron gaggawa na kwamitin a Abuja.

Sai dai, ya bayar da tabbacin cewa ba za a sami rikici a jam’iyyar ba kamar yadda ake hasashe a wasu wurare, koda kuwa kwamitin ya kasa shirya babban taron na kasa a watan Yuni.

Ana sa ran babban taron Jam’iyyar APC zai samar da sabbin shugabannin da za su ja ragamar jam’iyyar.

James, wanda tsohon sanata ne, ya ce kwamitin na duba batutuwa da dama tare da tuntuba sosai kafin ya yanke hukunci.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: