Jam’iyyar APC ta sanya ranar 24 ga Yuli domin gudanar da taron NEC na ƙasa don tantace shugaban jam’iyyar
Jam’iyyar APC mai mulki ta sanya ranar 24 ga Yuli domin gudanar da taron NEC na ƙasa don tantance makomar shugabancin jam’iyyar.
Wannan na zuwa ne bayan murabus da Abdullahi Umar Ganduje ya yi daga shugabancin jam’iyyar saboda rashin lafiya.
Ali Dalori, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar daga Arewa maso Gabas, ya hau kujerar shugaban riko.
Taron zai tattauna batutuwan shiryawa zaɓen 2027 da sauye-sauyen cikin gida.