Jam’iyyar APC Tayi Kira Ga Kotu Da Tayi Watsi Da Kararrakin Jam’iyyun Adawa

0 76

Jam’iyyar APC ta yi kira ga kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ke Abuja da ta yi watsi da karar da jam’iyyun adawa uku suka shigar na kalubalantar nasarar da dan takararta na shugaban kasa, Bola Tinubu ya samu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Jam’iyyar APC ta bukaci kotun da ta yi rangwame kan koke-koken, a cikin martani daban-daban guda uku da aka shigar a sakatariyar kotun jiya da daddare, ta hannun Thomas Ojo, memba a kungiyar lauyoyin jam’iyyar karkashin jagorancin Lateef Fagbemi, SAN.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ya bayar da rahoton cewa, jam’iyyun siyasar uku; AA, APM da Jam’iyyar APP, a wasu kararraki daban-daban, sun kalubalanci nasarar Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.
Jam’iyyar AA a cikin karar, ta maka hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, APC, Tinubu da Hamza Al-Mustapha, dan takarar shugaban kasa na bangarenta kuma tsohon dogarin ga marigayi Janar Sani Abacha.
A cikin kararrakin, AA da dan takararta na shugaban kasa, APM da APP suna kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa bisa zargin rashin bin dokokin zabe da kuma ka’idojin INEC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: