Jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa ta gudanar da zaben fidda gwani na yan takarar majalissar dokokin jiha da na majalissar wakilai ta kasa

0 78

Jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa ta gudanar da zaben fidda gwani na yan takarar majalissar dokokin jiha da na majalissar wakilai ta kasa a fadin jihar.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Jigawa Babandi Ibrahim Gumel ne ya bayyana hakan, a lokacin dayake zantawa da manema labarai.

Ya kuma yabawa jagoran jam’iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule bisa taimakawa da daidaita jam’iyyar PDP dayake yi.

Babandi ya kuma ce an gudanar da zaben fidda gwanin ne ta hanyar sasanto.

Ya kara da cewa masu zaben yan takarkarun wato Deligates sunhada hadu ne a hedikwatar mazabu 30 na Yan majalissar dokokin jiha, bayan sasanto suka Garzaya zuwa hedikwatar yan majalisar wakilai 11 dake jihar nan.

Babandi Ibrahim Gumel Ya kuma yabawa Deligates, Jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Jamian tsaro da kuma Yan Jaridu bisa sanya ido a zaben a aka gudanar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: