Jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnan babban bankin kasa yayi murabus cikin gaggawa

0 89

jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnan babban bankin kasa (CBN), Godwin Emefiele yayi murabus cikin gaggawa.

Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan, yayin da yake zantawa da manema labarai yau a Sakateriyar Jam’iyyar ta Kasa a Abuja, ya ce wa’adin Emefiele a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, a karkashin gwamnatin jam’iyyar APC an samu koma baya sosai a manufofin kudi da na kasafin kudi, wanda hakan ya jawo bukatar saukarsa daga mukamin. Ologbondiyan ya ce abu ne mai muhimmaci a lura cewa lokacin da Godwin Emefiele ya hau kujerar Gwamnan Babban Bankin Kasa a shekarar a 2014 ana canza Dalar Amurka daya akan naira 164, amma a yanzu ana canja ta akan naira 575.

Leave a Reply

%d bloggers like this: