Jam’iyyar PDP ta kalubalanci shugaba Buhari bisa kin bayyana masu daukar ta’addanci a Najeriya

0 83

Babbar Jam’iyar Adawa ta Kasa wato PDP ta kalubalanci Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kan kin bayyana sunayen mutanen da suke daukar nauyin ta’addanci da kuma yan bindiga a kasar nan.

Jam’iyar PDP na mayar da raddin ne, biyo bayan Jawabin Mai Magana da yawun Shugaban Kasa Mista Femi Adesina, wanda ya ce Gwamnatin tarayya bata da niyar bayyana sunayen masu daukar nauyin yan ta’adda.

Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, ta sanya sunayen wasu yan Najeriya 6 masu daukar nauyin ta’addanci.

Da yake zantawa da gidan Talabijin na Channels Tv, Femi Adesina, ya ce gwamnatin tarayya tafi mayar da hankali kan hukunta mutanen sabanin bayyana sunayen su.

Amma cikin wata sanarwa ta Kakakin Jam’iyar PDP Mista Kola Ologbondiyan, ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta kwarance wajen kin yin Allah wadai da ayyukan ta’addanci a kasar nan.

PDP ta ce gwamnatin APC bata da wani abun boyewa, saboda haka yana da matukar muhimmanci gwamnatin tarayya tayi gaggawar bayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci kamar yadda Dubai ta aikata hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: