Jam’iyyar PDP reshen Jihar Jigawa ta sha alwashin dawowa kan karagar mulki a zaɓen 2027 tare da fitar da ‘yan ƙasa daga halin ƙunci da suka tsinci kansu aciki.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Umar Kyari Jitau ya fitar, PDP ta ce zarge-zargen da dan takarar jam’iyyar NNPP na 2023, Aminu Ibrahim Ringim ke yi, ba su da tushe kuma na siyasar ɓacin rai ne.
PDP ta ce Aminu Ringim na ƙoƙarin jawo hankali daga sakamakon zaɓen da ya nuna rashin amincewa da shi da jam’iyyarsa daga jama’a.
Jam’iyyar ta bukaci magoya bayanta da su mai da hankali kan muradunsu, ba kan “surutun ɗan siyasar da ya ƙare ba”.