Japan za ta taimakawa ƙananan ma’aikata a Najeriya domin samar da shinkafa

0 121

Gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar da za ta taimaka wajen samar da irin shinkafa mai inganci tsakaninta da Japan.

Ministan kasafin kudi da tsare-tsare Atiku Bagudu ne ya sanya hannun a madadin gwamnatin kan yarjejeniyar.

Ya ce Japan ta cimma abubuwa da dama ta bangaren aikin noma musamman samar da shinkafa da kuma noma ta hanyar fasaha.

Japan ta ce za ta taimakawa ƙananan ma’aikata domin su samar da shinkafa ma’ana su mori ƙasar da suke rayuwa a cikinta.

Babban burin shi ne taimakawa kowa a Najeriya, amma musamman kananan manoma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: