Jerin manyan bakin da suka halarci auren Yusif Buhari da Zahra Bayero

0 98

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na daga cikin jiga-jigan mutanen da suka je masarautar Bichi ta jihar Kano, lokacin da Yusuf Buhari, dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya auri Zahra Bayero diyar sarkin.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Ali Isa Pantami, ya daurawa ma’auratan aure a babban Masallacin Bichi bayan an biya naira dubu 500 a matsayin sadaki.

Dan dan’uwan Shugaba Buhari, Malam Maman Daura, shine waliyyin ango, a madadin shugaban kasa, yayin da fitaccen dan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, ya zama waliyyin amaryar a madadin dangin Bayero.

Manya manyan mutane sun halarci daurin auren, wanda aka shafe tsawon makonni ana zancensa.

Gwamnoni, ministoci, sanatoci da manyan ‘yan kasuwa maza da mata sun kasance a Bichi domin bikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: