Jerin Sunayen yan masarautar Kano da EFCC ke tuhumar su

0 231

A ranar Litinin 19 ga watan Afrilun 20201 ne hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da karɓar ƙorafe-ƙorafe ta Kanoa arewacin Najeriya, ta bayar da belin Awaisu Abbas Sanusi mataimakin sakataren masarautar Kano.

Haka zalika ta tsare Kabiru Sarki Waziri ɗa ga Dan Rimin Kano kan gazawarsa wajen bayar da bayanai kan yadda aka siyar da filayen unguwar Dorayi Ƙarama wato filin gidan Sarki.

A ranar Litinin ne dai hukumar ta nemi Awaisu Abbas Sanusi da Kabiru Sarki Waziri da Isa Bayero da aka fi sani da Isa Pilot, da su bayyana a hukumar da misalin ƙarfe 11 na safiyar Litinin, don amsa tambayoyi kan yadda aka cefanar da filayen Gidan Sarki na Dorayi Ƙarama.

Hukumar ta ce ta bayar da belin Awaisu Abbas Sanusi kan sharaɗin riƙe fasfonsa na fita kasashen waje, sannan ya kawo wanda zai tsaya masa, kuma ya kasance ɗan majalisar Sarkin Kano.

Ga dai jerin sunayen wadan hukumar ke tuhuma da kuma alaƙarsu da masarautar

Awaisu Abbas Sanusi

Shi ne mataimakin magatakarda (sakataren) na Masarautar Kano, kuma ɗa ne ga Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi, wanda shi ne babban dan majalisar Sarkin Kano.

Awaisu ɗan uwa ne ga shugaban jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano Abdullahi Abbas.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da karɓar ƙorafe-ƙorafe na bincikensa ne kan wasu takardun cinikin filin da suka nuna ya sa hannu ya karɓi dala 416,000 na filin Gidan Sarki na Dorayi Ƙarama.

Tana kuma son jin bayani kan yadda aka yi ba a sa kudin a asusun Masarautar Kano ba, duk da cewar yana da masaniyar cewa filin na Masarautar Kano ne.

Sannan ana bincikensa da fito da bayanan da ya sani a kan cinikin filayen.

Kabiru Sarkin Waziri

Ɗa ne ga Ɗan Rimin Kano, ɗaya daga cikin manyan masu muƙami a Masarautar Kano.

Hukumar na bincikensa ne a matsayinsa na wanda ya kawo Alhaji Yusuf da ya sayi filin da ake dambarwa a kai.

Sannan akwai wata takarda da ke nuni da aka ce mahaifinsa ne ya sa mata hannu, shaidar cewa an sayar da filin.

Sai dai daga bisani hukumar ta ce sa hannun na bogi ne ba na Ɗan Rimin Kano ba ne, sannan ga shi ba shi da lafiya balle ya zo gaban hukumar.

Isa Sanusi Bayero

Shi ne tsohon sakatare na musamman ga marigayi Sarki Ado Bayero da Sarki Sanusi na II, kuma kawu ga tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi, da sarkin Kano na yanzu Alhaji Aminu Ado Bayero.

Hukumar na zarginsa da karbar kudin da aka sayar da filayen Gidan Sarki na Ɗorayi Ƙarama, da ke Gwale.

Sannan suna bincikensa yadda aka yi da kudin, ina aka kai su, da dalilin da ya sa ba a saka kudin a asusun Masarautar Kano ba.

Sannan tana zarginsa da bai wa ɗan wansa Awaisu Abbas Sanusi, da ya sa hannun a takardar cinikin filayen na Ɗorayi Ƙarama.

Tana kuma zarginsa da bai wa Kabiru Sarki Waziri da Awaisu Abbas Sanusi da saka hannu a takardun ciniki fillin, a madadinsa, tare da sa hannun bogi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: