Wani jirgin sama mallakin kamfanin sufuri na Air Indiya ya yi hatsari inda ya faɗa kan wata unguwa da ke birnin Ahmedabad a yammacin ƙasar Indiya.
Ana da yaƙinin cewa akwai aƙalla fasinjoji 200 da kuma ma’aikata a cikin jirgin.
Bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta ya nuna baƙin hayaƙi ya turnuƙe bayan rikitowar jirgin.
Yanzu haka ma’aikatan kashe gobara da masu bayar da agajin gaggawa sun garzaya wurin da lamarin ya faru.