Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya gayyaci shugaba Buhari taro tare da wasu shugabannin kasashen duniya.

Shugaba Buhari zai bayyana tare da shugabannin kasashen duniya ta yanar gizo, inda za su tattauna batun canjin yanayi da gudunmawar da kasashen duniya ke badawa.

Shugabannin da aka Biden ya gayyata sun hada da
Russia Vladimir Putin shugaban kasar Chana Xi Jinping, Jamus Angela Merkel, Faransa Emmanuel Macron Firaye Ministan Boris Johnson

Sauran sun hada da Sarkin Saudi Salman bin Abdulaziz, Brazil Bolsonaro, Indiya Narendra Modi da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Bayan shugaba Buhari akwai wasu shugabannin kasashen Afrika da suka hada da na Gabon Ali Bongo Ondimba, Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, Kenya Uhuru Kenyatta da na Félix Tshisekedi, Democratic Republic of the Congo.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: