Jonathan yace Ƴar’adua mutum ne mai kishin ƙasa da son mutane

0 179

Tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, ya ce za a ci gaba da tuna ubangidansa marigayi Umaru Musa Ƴar’adua a matsayin mutum mai son zaman lafiya.

Umaru Ƴar’adua ya rasu a ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2010, bayan fama da rashin lafiya a lokacin yana mulkin Nijeriya.

A ranar 6 ga watan ne kuma aka naɗa Jonathan a matsayin sabon shugaban ƙasar da ya gaji Ƴar’adua.

A saƙonnin da ya wallafa a twitter don tunawa da cika shekara 11 da rasuwar Ƴar’adua a ranar Larabar nan, Jonathan ya bayyana ubangidan nasa a matsayin mai son zaman lafiya, ci gaban ƙasa da sauƙin sha’ani, wanda ya jajirce wajen bauta wa ƙasa, nuna gaskiya da son al’umma.

Ya ce Ƴar’adua ya sadaukar da rayuwarsa wajen samar da daidaito a cikin al’umma har zuwa ƙarshen rayuwarsa.

Jonathan ya yi bayanin cewa Ƴar’adua mutum ne da za a ci gaba da tunawa da su har abada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: