Jumillar kudaden da ‘yan kwangila suke bin gwamnatin tarayya bashi domin ayyukan manyan hanyoyin da gadoji ya kai miliyan dubu 420 da miliyan 583

0 62

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, a jiya yace jumillar kudaden da ‘yan kwangila suke bin gwamnatin tarayya bashi domin ayyukan manyan hanyoyin da gadoji, zuwa ranar 20 ga watan Oktoban da ya gabata, ya kai miliyan dubu 420 da miliyan 583 da dubu 705 da naira 963 da kobo 48.

A cewarsa, hakan yana sanyaya gwiwar kokarin gwamnati wajen tsara sauran hanyoyin samun kudaden gudanar da ayyukan.

Yayi jawabi a Abuja lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin ayyuka na majalisar wakilai domin kare kasafin kudin badi na ma’aikatarsa.

Yace baya ga matsin da suke fuskantar na biyan kudaden, akwai karancin kudaden ayyuka da ake warewa a kasafin kudi, inda ake ware naira miliyan 100 ko miliyan 200 domin ayyukan titunan dake bukatar naira miliyan dubu 20 ko ma fiye da haka.

Yace ma’aikatarsa na aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin fara ayyukan gadojoji a tashoshin jiragen ruwan kasarnan da guraren ajiyar mai domin rage lalacewar tituna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: