Kakakin majalissar dokoki ta kasa ya shawarci masu rike da mukaman siyasa su gaggauta ajiye mukamansu idan suna son fitowa takara

0 56

Kakakin majalissar dokoki ta kasa Femi Gbajabiamila ya shawarci masu rike da mukaman siyasa su gaggauta ajiye mukamansu, inda yace bujerewa hakan, zai sanya soke zaben mutum, koda yasamu nasara.

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne a lokacin dayake zantawa manema labarai a kasar Birtaniya, a lokacin dayake gabatar da wata Makala.

A cewar sa sashi na 84, 12 cikin baka na sabuwar dokar zabe ta 2022, ta bayyana cewa dole ne, masu rike da mukaman siyasa su sauka daga mukamansu, idan har suna son tsayawa takarar zabe.

Ya kara da cewa, kadan ne daga cikin masu rike da wannan makaman ne kawp yanzu suka ajiye aikin su.

Wasu da dama haryanzu suna sar-sarfa akan matakin, wanda kuma zai iya sawa a rushe zaben mutum koda yasamu nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: