Kamfani mai na kasa NNPC ya kashe biliyan 100 a gyara matatun man Najeriya a 2021

0 48

Kamfanin man fetur na kasa, wato Nigerian National Petroleum Company (NNPC) ya bayyana cewa ya kashe naira biliyan 100 wajen gyaran matatun mai na ƙasa a cikin shekarar 2021 data gabata.

kamfanin na NNPC ya bayyana hakan ne cikin wani rahoton shekara da ya gabatar wa asusun haɗaka na gwamnatin tarayya da jihohi yayin wata ganawa..

Duk da cewa ba a bayyana matatun ba da aka gyra ba, NNPC ya ce ya kashe naira biliyan 8.3 a kowane wata na 2021 don gyara matatun man.

Matatun man da ke ƙarƙashin kulawar NNPC din sun haɗa da ta Fatakwal da Kaduna da Warri.

Baki ɗayansu, suna da ƙarfin tace gangar mai 445,000 duk rana, kuma duk da cewa Najeriya na da matatu huɗu, tana kai ɗanyen mai ƙasashen waje a tace sannan ta sayo tataccen don shigowa da shi cikin ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: