Kamfanin jiragen saman Najeriya mai suna Nigeria Air ya karbi lasisin sufurin jiragen sama domin fara aiki

0 85

Kamfanin jiragen saman Najeriya mai suna Nigeria Air, ya karbi lasisin sufurin jiragen sama domin fara aiki.

Da take tabbatar da hakan ta shafinta na Twitter a jiya, Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Kasa ta ce lasisin sufurin jiragen sama da Darakta Janar na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kasa, Kyaftin Musa Nuhu ya sanya wa hannu, zai yi aiki na tsawon shekaru biyar, daga ranar 3 ga watan Yunin da muke ciki zuwa 2 ga watan Yunin, 2027.

Wannan na zuwa ne shekaru hudu bayan kaddamar da kamfanin jiragen saman na kasa da ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya kaddamar.

An dakatar da fara aikin kamfanin jiragen ne biyo bayan kin biyan kudi dala miliyan 300 da ministan ya yi.

Sai dai, wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ruwaito ministan yana bayanin cewa dala miliyan takwas da gwamnatin tarayya za ta bayar shine jarin fara aiki domin samar da ofisoshi da sauran kayayyakin da ake bukata don fara jigilar jiragen saman.

Ya kara da cewa dalar Amurka miliyan 300 ita ce dukkan kudaden da ake bukata domin tafiyar da kamfanin jiragen saman na tsawon shekaru uku.

Leave a Reply

%d bloggers like this: