Kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO ya bayyana cewa za’afuskanci karancin wutar lantarki

0 126

Kamfanin rarraba wutar lantarki na shiyyar Kano, Jigawa da Katsina KEDCO ya bayyana cewa za’afuskanci karancin wutar lantarki a Jihohin.

Wannan a kunshe cikin wata takarda da jami’in yada labarai na kamfanin Ibrahim Sani Shuwa ya rabawa manema labarai a yau.

Inda yace mahukunta kamfanin sun bayyana hakan ne bayan an rage yawan wutar da ake bawa yankin daga MegaWatt 365 zuwa MagaWatt 238, wanda ya rage yawan wutar da ake bukata a kullum.

Ya kara da cewa yanzu haka sunfara gudanar aikin layin samar da wutar Makurdi Zuwa Jos da ake sa ran samun KiloVat 330 wanda ake tsammanin kammalawa nan da 9 ga watan Oktoba na wannan shekarar.

Anasa bangaren babban daraktan tsare tsaren kamfanin David Omoloye, ya bukaci al’umma suyi hakuri su rage amfani da wuta barkatai tare da chanchanta wutar lantarki da suke amfani da ita a kullum.

Inda yakara da jan hankalin mutane akan suke kashe abubuwan da suke amfani da wutar lantarki daga zarar sun kammala aiki da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: