Karamar hakuma kafin hausa tace ta sayi kayan famfunan tuka-tuka da kudin su ya kai naira miliyan 50 a watanni 7 da suka gabata.

Shugaban karamar hukumar Alhaji Saminu Yahaya ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a dutse babban birni jiha.

Yace cikin famfuna dubu 4, an gyara sama da dubu 3 da 500.

Karamar hukumar ta gyara famfuna a garurun Bulangu, da kafin hausa na sama da naira miliya 1

Alhaji Saminu Yahaya yayi jawabin cewa an zamantar da tuka-tukan garuruwan sarawa da shakato zuwa masu amfani da hasken rana, akan kudi sama da naira miliyan 8.

Kazalika karamar hukumar ta raba kayayyakin aikin lafiya na sama da naira miliyan 2 a asibitocin Dumadumin Toka, Dumadumin Kyaure, Mezan da Ruba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: