Kasar Habasha na shirin kwaso ‘yan kasarta su dubu 100 da ake tsare da su a gidajen yari a kasar Saudiyya.

Ana zargin da yawa daga cikinsu sun shiga kasar ne ba bisa ka’ida ba kuma ba su da wasu takardu da za su yi aiki a can.

Gwamnatin Habasha ta kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin bakin hauren.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce kwamitin ya tattauna da masu ruwa da tsaki kan yadda za a tafiyar da lamarin.

Wata jami’ar ma’aikatar, Birtukan Ayano, tace za ayi kokarin sauya rayuwar wadanda aka kwaso ta hanyar basu horo.

Fursunonin sun shaida wa manema labarai cewa, suna fuskantar tauye hakkin bil’adama da suka hada da rashin abinci da rashin ruwan sha mai tsafta da kuma rashin ayyukan kiwon lafiya.

Hotunan da ake ta yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna fursunonin cikin wani dan karamin daki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: