Kasar Najeriya ta karbi ‘yan gudun hijarar Kamaru tare da yi musu rijisata su 73,000

0 68

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijara da ‘Yan Cirani ta Najeriya, ta ce ta karbi ‘yan gudun hijarar Kamaru tare da yi musu rijisata su 73,000.

Manema labarai sun ruwaito Kwamishinar Hukumar, Iman Sulaiman-Ibrahim ce ta bayyana hakan a makon da ya gabata a wani taron kara wa juna sani game da yi wa ’yan gudun hijira da masu neman mafaka rijista a Abuja.

Ta ce Rikicin siyasar Kamaru ya ki ci ya ki cinye wa tun 2016, kuma hakan ya janyo karuwar cin zarafin dan adam tare da asarar rayuka da dukiyoyi musamman a yankuna biyu na arewa maso yamma da kuma kudu maso yamma na kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: