Kasar saudiyyar ta dage takunkumin data kakabawa Nigeria na hanata shiga kasar saboda cutar corona, ta kuma tabbatar da cewa janyewar zata fara aiki ne tindaga ranar 5 ga wannan watan na Maris.

Hukumar jindadin alhazai ta kasa NAHCON ce ta bayyana hakan, ta bakin jami’in yada labaran hukumar Fatima Sanda-Usara, wacca ta wallafar takardar shaidar dage dokar wacca suka samu daga hukumar kula da aikin hajjin kasar saudiyyan.

A cewar sanarwar, hakan ya biyo bayan cire wasu daga cikin takunkuman kariya daga cutar ne da kasar saudiyyan tayi, wanda ta tabbatar da cewa yanzu haka za’adawo aikin hajji da ummarh kamar yanda aka saba a baya.

Amma sanarwar ta kara da cewa, dole ne mutum ya gabatar da takardar shaidar karbar alluarar rigakafin corona kafin ya shiga cikin kasar.

Anasa bagaren shugaban hukumar jindadin alhazai ta kasa NAHCON Zikrullah Kunle-Hassan ya yabawa kasar saudiyyar bisa daukan wannan matakin tare da godewa Allah bisa dawowar gudanar da ibada a masallatan Makkah da Madina masu tsarki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: