Kasar Sin ta aika dakarun wanzar da zaman lafiya sama da dubu 50 tun daga 1990

0 73

Jiya 29 ga watan Mayu, rana ce ta jami’an wanzar da zaman lafiya ta MDD. Taken ranar a bana shi ne “hanya mai dorewa ta wanzar da zaman lafiya: sa kaimi ga matasa domin taka rawa wajen shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali”.

Kasar Sin ita ce babbar kasa ta biyu dake biyan kudin tallafi da kudin karo karo ga MDD, kuma ita ce kasar da ta fi kowacce ba da adadi mai yawa na dakarun wanzar da zaman lafiya, tun daga shekarar 1990. Wato bayan kasar ta shiga aikin kiyaye zaman lafiya na MDD, sai da sojoji da ‘yan sandanta suka shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya har sau 30. Haka kuma, ta aike da dakarun da yawansu ya kai sama da dubu 50, cikin shekaru 30 da suka gabata. Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin suna gudanar da ayyukan daidaita rikici da kiyaye kwanciyar hankali da kuma ingiza ci gaban tattalin arziki a kasashe da yankuna sama da 20, ciki har da Cambodiya, da Kongo(Kinshasa), da Liberiya, da Sudan, da Lebanon, da Sudan ta kudu, da Mali, da Afirka ta tsakiya da sauransu.

A halin yanzu, jami’an wanzar da zaman lafiya na kasar Sin sama da 2500 suna ci gaba da gudanar da ayyuka a wurare 8 da kuma hedkwatar MDD.(Jamila CRN).

Leave a Reply

%d bloggers like this: