China ta sanar da cewa za ta ƙyale duk ma’aurata su haifi yara uku, abin da ya kawo ƙarshen tsattsaurar dokar da ta sharɗanta haihuwar yara biyu.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Xinhua mallakar ƙasar, an ɗauki matakin ne bayan wani taro a ranar Litinin.

Wannan na zuwa ne bayan wasu alƙaluman ƙidaya da suka nuna cewa al’ummar ƙasar ba ta ƙaruwa yadda ya kamata.

Hakan ya sa China ta ƙara ɗaukar matakai na sake ƙarfafa wa ma’aurata gwiwar haihuwar yara domin guje wa raguwar al’umma.

Raguwar al’umma matsala ce musamman saboda tsofaffi na fin matasa yawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: