Kasar Turkiyya ta dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci da Isra’ila

0 58

Turkiyya ta ce ta dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci da Isra’ila dangane da yaƙin da ake yi a Gaza, saboda taɓarɓarewar yanayin jin ƙai a yankin.

An dai yi ƙiyasin adadin cinikayyar tsakanin ƙasashen biyu ya kusan dala bilyan bakwai a bara.

Ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta Turkiyya ta ce za a aiwatar da matakin har sai Isra’ila ta bayar da damar shigar da kayan jin ƙai zuwa Gaza ba tare da matsala ba.

Ministan harkokin wajen Isra’ila ya zargi shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan da kasancewa kamar mai mulkin kama karya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: