Kashim Shettima ya bayyana ɗan kasuwan Najeriya Dangote a matsayin baƙar fata mafi tasiri da ƙima a duniya
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana ɗan kasuwan Najeriya kuma attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, a matsayin baƙar fata mafi tasiri da ƙima a duniya cikin shekaru 300 da suka wuce.
Shettima ya bayyana hakan ne a yayin bikin taron zuba jari na Taraba mai taken ‘Taravest’, wanda aka gudanar a garin Jalingo, babban birnin jihar.
Wannan yabo na Shettima ya biyo bayan saka sunan Dangote a jerin TIME100 Philanthropy na mujallar duniya ta TIME Magazine, wanda ke bayyana mutane 100 da suka fi tasiri wajen aikin jin ƙai a duniya.
Aliko Dangote ne kaɗai Ɗan Najeriya da ya samu wannan gagarumar lamba a shekarar 2025, kuma an saka shi a rukunin “Titans” – inda ya shiga jerin sunayen manyan mutane irin su Michael Bloomberg, Oprah Winfrey, Warren Buffett, da Melinda Gates.
A yayin taron, Shettima ya yabawa Dangote bisa kaunar ƙasa da sadaukarwa, musamman ganin yadda ya kafa matatar mai mafi girma a Afirka, wadda ake fatan za ta taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya. A nasa bangaren, Dangote ya ce, aikin jin ƙai ya fi kasancewa aikin da yafi jin dadi fiye da na kasuwanci, yana mai tabbatar da cewa ya himmatu wajen ganin Afirka ta tsaya da kafarta.