Kashim Shettima ya roƙi Isra’ila ta rungumi matasan Najeriya domin ta ciyar da su gajiyar shirin i-FAIR

0 129

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya roƙi gwamnatin Isra’ila ta faɗaɗa shirin Tallafa Wa Matasa a Fannin Ƙirƙira da Bincike na i-FAIR.

Shettima ya yi wannan kira a lokacin da ya ke kewayen gani da ido a cibiyar Inmov8Hub, tare da Babban Daraktan Ma’aikatar Harkokin Wajen Isra’ila, Yaakov Blitshien, ranar Lahadi, a Abuja.

Shettima, wanda ya samu wakilcin Mashawarcin Musamman kan Fannin Tattalin Arziki na Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Tope Fasua, ya jinjina wa shirin i-FAIR, wanda ƙasar Isra’ila ta ɗauki nauyi, domin matasan Najeriya su ci gajiyar shirin.

Ya ce kamata ya yi a faɗaɗa shi sosai, ta yadda za a rungumi matasa masu tarin yawa.

Shettima ya ce, “I na tunanin wasu abubuwan da aka bijiro da su da muke gani a nan, za su amfani matasan mu sosai. Kuma matasa da dama sun ɗauki saitin magance wa kan su matsalolin da ke addabar su.

“Ga dai fuskokin tsadar abinci da ke addabar kowa, har ta ƙaru da kashi 40 bisa 100, wadda ba abin da za a zuba ido ba ne ana kallo. Shi ya sa muke ta ƙoƙarin lalubo hanyoyin magance matsalolin.”

Shi kuwa Blitshien cewa ya yi shirin i-FAIR na ɗaya daga cikin tsare-tsaren da Isra’ila ta fara a Najeriya, wanda ya ce ya samu gagarimar nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: