Kashim Shettima yayi kira ga likitoci dasu dena fita ƙasashen waje don neman aiki

0 104

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga likitocin ƙasarnan, su riƙa zama a ƙasar, don taimaka wa magance matsalar da ƙasar ke fuskanta ta ƙarancin likitoci.

Shettima ya yi kiran ne a lokacin da ƙungiyar likitocin ƙasar – ƙarƙashin jagorancin sabon shugabanta, Farfesa Bala Audu – suka kai masa ziyara a ofishinsa ranar Talata.

Mataimakin shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda likitocin ƙasar ke yawan ficewa daga ƙasar domin neman ayyuka a ƙasashen waje.

A baya-bayan nan dai ana samun yawaitar ficewar likitocin Najeriya daga ƙasar, zuwa ƙasashen wajen domin samun ingantaccen albashi da yanayin aikin mai kyau.

Sai dai mataimakin shugaban ƙasar, ya jaddada cewa gwamnatinsu na iya bakin ƙoƙarinta wajen inganta yanayin aikin likitoci a ƙasar, musamman waɗanda suka zaɓi tsayawa su yi aiki a ƙasar. 

Leave a Reply

%d bloggers like this: