Kaso 99 na yan takarar shugaban kasa sun amince da yin sasanto wajen fidda yan takara – APC

0 126

Shugaban Kwamatin Tantance Yan Takarar Shugaban Kasa a Jam’iyar APC John Oyegun a jiya ya ce kaso 99 na yan takarar shugaban kasa sun amince da yin sasanto wajen fidda yan Takara.

Mista Oyegun, ya bayyana hakan ne lokacin da yake mika rahotan sa ga Shugaban Jam’iyar na Kasa Malam Abdullahi Adamu.

A cewarsa, sun tuntubi yan takarkarun kan sasanto, inda kaso 99 na cikin su suka amince da cewa Jam’iya ita ce sama da kowa, tare da yin Alkawarin cewa zasu yiwa Jam’iya biyayya.

Haka kuma Mista Oyegun ya ce daga cikin yan Takara 23, 10 daga cikin su basu cancanci tsayawa Takara ba.

John Oyegun, ya ce yan Takara 13 ne kawai suka cancanchi tsayawa Takara.

Sai dai Mista Oyegun bai bayyana sunayen mutanen da suka cancanchi tsayawa takarar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: