Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin majalisun kasa, Hon Abdurrahman Kawu Sumaila, ya fice daga jam’iyyar APC.

Kawu Sumaila, wanda kuma tsohon dan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazabar Sumaila da Takai a jihar Kano, yace yayi iya bakin kokarinsa a jam’iyyar amma lokaci yayi da ya kamata ya fice.

An ce Kawu Sumaila ya kammala shirin shiga sabuwar jam’iyyar NNPP bayan ya gana da shugaban jam’iyyar na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso.

A wani batun kuma, tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru da Bebeji a jihar Kano, Abdulmuminu Jibrin Kofa, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar NNPP.

A karshen makon da ya gabata ne Abdulmuminu Jibrin Kofa, ya sanar da matakin ficewa daga jam’iyyar APC inda ya ce zai bayyana jam’iyyar da zai koma cikin sa’o’i 24.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: