KEDCO ta kara samar da wutar lantarki ga Jihohin Jigawa da Kano da Katsina a wani mataki na tabbatar da jin dadin abokan huldarsa

0 112

Manajan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki shiyyar Kano (KEDCO) a jiya ya ce ya kara samar da wutar lantarki ga dukkan abokan huldarsa a Jihohin Jigawa, Kano da Katsina, a wani mataki na tabbatar da jin dadin abokan huldarsa.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a yau dauke da sa hannun Ibrahim Sani Shawai, shugaban sashen sadarwa na kamfanin.

Sani Shawai ya bukaci kwastomomi a jihohi daban-daban da su bunkasa dabi’ar biyan kudin wutar lantarki gaba daya, inda ya bayyana cewa irin wannan biyan akan kari zai taimakawa kamfanin don cigaba da kokarin da yake yi wajen tabbatar da ingantaccen aiki.

Sai dai, duk da haka, ya koka kan cewa matsalolin rashin biyan kudi da ma biyan kudi da kadan-kadan, wanda ya ce kusan sun zama ruwan dare, yana kawo cikas ga ayyukan kamfanin don gamsar da abokan hulda da masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: