Kimanin kwanaki 5 kenan a jere ƴan bindiga a jihar Zamfara na cigaba da tare manyan hanyoyin sufuri na Jihar

0 147

Kimanin kwanaki 5 kenan a jere, Yan Bindiga a Jihar Zamfara na cigaba da tare manyan hanyoyin Sufuri na Jihar, a cewar mazauna wasu kyauyika na yankin.

Mazauna Karkarar sun yan bayyana Gidan Talabijin na Channels Tv, cewa matsalolin tsaro na cigaba da ta’azzara a hanyoyin da suka hada Kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi da kuma Kauran Namoda, inda suka kashe Matafiya 6.

Majiyoyin sun ce yan bindigar da suka tare hanyoyin sun nuna damuwar kan rufe Kasuwar Shanu ta Shinkafi, inda suka sa ce Matafiya tare da kone wasu Motoci.

Hukumomin tsaro na Jihar duk da cewa sun tabbatar da gaskiyar faruwar lamarin, amma sun bayyana cewa kawo yanzu Jami’an tsaro sun dawo da zaman Lafiya a hanyar ta Shinkafi–Moriki–Kaura-Namoda.

Wani mazaunin garin Shinkafi Malam Aliyu Guraguri, ya fadawa gidan Talabijin na Channels Tv cewa, yan bindigar sun fusata kan matakin da gwamnati ta Dauka na rufe Kasuwar Dabbobi ta Shinkafi, inda suka bayyana cewa babu wanda zai ci wata Kasuwa a Karamar Hukumar ta Shinkafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: