Kimanin maniyyata aikin hajji dubu 1 da 165 ne suka biya kudin ajiya ta hannun hukumar jin dadin alhazai ta Jihar Jigawa daga shekara ta 2020 zuwa 2021.

Mukaddashin sakataren zartarwa na hukumar, kuma daraktan kudi da mulki na hukumar, Alhaji Mustapha Umar ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse.

Ya ce sakamakon annobar cutar korona da ta jawo rashin zuwa aikin hajji, ya sanya daga cikin adadin, maniyyata 638 ne suka nemi hukumar ta mayar musu da kudaden ajiyar su, inda yace a saboda haka ne hukumar ta kafa kwamatin da zai warware matsalalolin.

Mustapha Umar ya bayyana cewa hukumar kula da aikin hajji ta kasa tuni ta umarci hukumomin jin dadin alhazai na jihohi da su dora maniyyata kan tsarin adashen gata na hukumar ta kasa.

Haka kuma hukumar ta gudanar da taro da kwamitocin kula da ayyukan aikin hajji tare da bita ga maniyyata da suka fito daga kananan hukumomi 27 na wannan jiha.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: