Kimanin mutane 10 aka kashe tare da raunata wasu 24 bayan wasu harbe-harbe da aka gudanar a Amurka

0 77

Kimanin Mutane 10 ne aka kashe tare da raunata wasu mutane 24, bayan wasu harbe-harbe 4 da aka gudanar cikin karshen makonnan a Amurka, a daidai lokacin da yan Majalisar kasar ke kokarin sanya dokar rage amfani da bindigogi barkatai a Kasar.

Yawan harbe-harben da ake samu da kuma kashe a kasar ya sanya ana yawan kiraye-kirayen sake yin dokoki kan amfani da bindiga a kasar.

Shugaban yan sandan yankin da lamarin ya faru Chief Celeste Murphy, ya ce kimanin mutane 14 aka harba a lokacin daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: