Labarai

Kimanin mutane 146 ne daga cikin fasinjoji 362 dake cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wayar su bata shiga bayan sati da harin yan bindiga

Kimanin mutane 146 ne daga cikin fasinjoji 362 dake cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wayar su bata shiga a halin yanzu, kwanaki shida bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin.

Manajan daraktan hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya, Mista Fidet Okhiria, shine ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar a safiyar yau Litinin.

Sai dai ya ce adadin fasinjojin da suka tsira ya karu zuwa 186.

Okhiria ya ce lambobin waya 51 da ke cikin takardar fasinjojin da aka samu a kashe suke.

Amma lambobin waya 35 da ke cikin takardar idan aka kira tana shiga amma ba’adauka.

Shugaban ya kuma kara da cewa kimanin mutane 22 ne ‘yan uwansu suka bace, sannan kuma an tabbatar da mutuwar mutane takwas.

Idan zamu iya tinawa dai Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya bayar da rahoton  yanda ‘yan ta’adda suka kai harin bama-bamai akan jirgin kasa Abuja zuwa Kaduna jirgin da ke cike da fasinjoji a daren ranar Litinin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: