Kimanin mutane 1,593 ne suka mutu sakamakon haɗurra a cikin wata ukun farko na shekarar 2025

0 210

Hukumar Kiyaye Aukuwar Haɗurra ta kasa, (FRSC) ta ce kimanin mutum 1,593 ne suka mutu sakamakon haɗurra a cikin wata ukun farko na shekarar 2025.

Cikin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna samun ƙaruwar munanan haɗurran da suka haddasa rasa rayuka da raunuka.

Hukumar ta bayar da rahoton cewa an samu haɗurra 2,650 a faɗin Najeriya daga watan Janairu zuwa Maris.

To sai dai bisa ga alƙaluman an samu raguwar yawan haɗuran idan aka kwatanta da daidai wannan lokacin a 2024.

Haɗurran ababen hawa na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da asarar rayuka a Najeriya, wani abu da masana ke alaƙantawa da rashin kyawun titunan ƙasar, da kuma tuƙin ganganci daga ɓangaren direbobi. Bayanai dai sun bayyana karuwar haduran ababen hawa akan titunan kasar nan dake cigaba da lakume rayuka da dukiyoyin jama’a.

Leave a Reply