Kimanin mutane 2 ne suka mutu biyo bayan wani haɗarin mota da ya afku a jihar Bauchi

Kimanin mutane 2 ne suka mutu a jiya, biyo bayan wani hadarin mota da ya afku a Jihar Bauchi.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Afkuwar Hadura ta Kasa reshen Jihar Bauchi Mr. Yusuf Abdullahi, shine ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce mutane 6 ne suka samu raunika a lokacin hadarin.
Haka kuma ya ce hadarin ya shafi wata motar haya guda 1 a kasuwar Durum wanda take kan hanyar Bauchi zuwa Kano.
Kwamandan ya ce mutane 8 ne hadarin ya shafa wanda suka hada da Maza 5 da Mata 2 da kuma karamin Yaro.
A cewarsa, hadarin ya faru ne saboda gudun wuce sa’a a tsakanin motocin hayar, wanda hakan ke haifar da asarar rayuka.
Kazalika, ya ce an kai Direban Motar zuwa Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa na Jihar Bauchi.