Kimanin Mutane 200,000 Yan Asalin Jihar Borno Ke Yin Gudun Hijira a Nijar

0 167

Kimanin mutane 200,000 yan asalin jihar Borno da ke gudun hijira a jamhuriyar Nijar mai makwabtaka, za’a dawo dasu gida a watan Mayu, wadanda suka bar gidajen su tun shekarar 2014 sakamakon rikicin kungiyar Boko.
Gwamnan jihar Babagana Zulum, shine ya sanar da haka jiya a Malam-Fatori dake karamar hukumar Abadam helkwatar iyakokin Tarayyar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.
Zulum yace yaje Malam-Fatori ne domin ya ganewa idon sa halin da garin yake ciki, da kuma bada goyan baya ga dakarun sojin Najeriya a shirin aikin dawo da yan Najeriya dake gudun hijira a Jamhuriyar Nijar domin maida su gidajen su na asali.
Babagana Zulum yace zai bada dukkan goyan bayan da ya kamata ga sojojin Najeriya domin ganin wannan aikin ya tabbata.
Gwamnan jihar yayi kira ga masu gudun hijirar da su bada cikakken hadin kai ga jami’an tsaro domin dawo dasu gida lafiya.
Zulum wanda ya gana da kwamandan bataliya ta 68 dake Malam -Fatori Canal A Onyeukwu, tare da rakiyar zababben dan majalisar mai wakiltar Marte,Monguno da Nganzai, Bukar Talba, da kuma kwamishinan kananan hukumomi,kula da masarautu Sugun Mai Mele da kuma wasu sanannun mutane yan asalin garin Abadam.

Leave a Reply

%d bloggers like this: