Kimanin mutane 46 ne aka bada rahoton sun mutu biyo bayan wata arangama a kasar Madagascar

0 70

Kimanin mutane 46 ne aka bada rahoton sun mutu, biyo bayan wata arangamar da mutanen wasu kauyuka suka yi da masu satar shanu a Madagascar.

An kai harin ne a yankin Marovitsika wanda ke kudancin kasar.

Bayanai sun ce mahara kusan 120 ne dauke da manyan makamai suka dirarwa jama’ar kauyen da na kewayensa.

Hukumar kare hakkin dan adam ta kasar ta ce za ta kaddamar da bincike mai zaman kansa a kan yadda lamarin ya faru.

Dama an jima ana samun rikici tsakanin barayin shanu da mazauna kauyukan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: