Kimanin mutane dubu 20 ke fuskantar cizon macizai a kowacce shekara a kasar nan

0 80

Wata sanarwa ta baya-bayan nan da karamin ministan lafiya Olorunnimbe Mamora ya fitar, bayyana cewa kimanin mutane dubu 20 ke fuskantar cizon macizai a kowacce shekara a kasar nan, wanda hakan na ciwa gwamnatin tarayya tuwo a kwarya.

A cewar Mamora Macijin dayafi cizon mutane shine Tandara, wanda yake cizon kaso 90 cikin 100 na adadin wadanda macizan ke ciza

kuma kaso 60 cin 100 na wadanda yake cizo ne suke mutuwa har Lahari.

Yawaitar samun rahotanni cizon macizai dai ya yawaita a kasar nan saboda faduwar damuna, da ake samun ruwa akai akai, wanda so da dama cizon ke jawo asarar rayuka.

Ya kara da da cewa Jihohin da akafi samun wannan rahotannin sunhada da Gombe, Plateau, Adamawa, Bauchi, Borno, Nasarawa, Enugu, Kogi, Kebbi, Oyo, Benue, and Taraba.

A cewar rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO, mutane da dama suna mutuwa sanadiyyar cizon macizai, wanda akalla ke daukar kaso 12 cikin 100 na yawan mutanen da suke mutuwa a kowacce shekara a fadin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: