Kimanin mutane dubu 500 ne ambaliyar ruwa ta shafa a jihohi shida na kasar Sudan ta Kudu

0 81

Kimanin mutane dubu 500 ne ambaliyar ruwa ta shafa a jihohi shida na kasar Sudan ta Kudu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Jihohi shida da annobar ta fi shafa sun hada da Jonglei a yankin gabashin kasar, da Western Equatoria, da Warrap, da Bahr El-Ghazal ta Arewa, da jihohin biyu masu arzikin mai na Unity da Upper Nile a arewacin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ambaliyar ruwan ta raunana garuruwa da kauyuka, inda mutane da yawa da suka rasa muhallansu ke neman mafaka a majami’u da makarantu.

Majalisar ta Dinkin Duniya ta ce mutanen da abin ya shafa na bukatar matsuguni na gaggawa, da harkokin kiwon lafiya da kayan abinci, da sauransu.

Ambaliyar tazo ne bayan ruwan saman da aka yi ta yi a farkon damina wanda ya haifar da ambaliyar Kogin Nilu tare da mamaye gonaki da kauyuka.

Ana hasashen karin ruwan sama mai yawa da ambaliya a watanni masu zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: