Kimanin mutum 1,100 ne ake sa ran za su amfana da tallafin gwamnatin tarayya a karamar hukumar Hadejia

0 170

Kimanin mutum dubu daya da dari daya ne ake sa ran za su amfana daga aikin raba kayan agaji a karamar hukumar Hadejia.

Mai bawa gwamna shawara na musamman kan bada agajin gaggawa Abdulwahab Toro Suleiman ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayayyakin.

Ya ce za a raba buhun shinkafa 550 ga masu karamin karfi a yankin.

A cewarsa mutane biyu za su karbi buhun shinkafa guda daya domin rage musu radadin da suke ciki a wani bangare na tallafin da gwamnatin tarayya ke samu ta shirin samar da abinci.

Da yake jawabin godiya shugaban karamar hukumar Hadejia Alhaji Ahmed Abba Ari ya yabawa gwamnati bisa wannan karimcin tare da jan kunnen wadanda suka amfana da su yi amfani da kayan yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: