Kimanin mutum dubu 20 macizai ke sara a duk shekara a fadin Najeriya

0 107

Kimanin Mutane dubu 15,000 zuwa dubu 20,000  Macizai ke sara a duk shekara a fadin kasar.

Karamin Ministan Ma’aikatar Lafiya ta Kasa Dokta Olorunnimbe Adeleke Mamora, shine ya bayyana hakan ga manema Labarai, inda ya ce mutane 479 ne macizai suke sara a cikin mutane dubu 100,000 a kasar nan duk shekara.

A cewarsa, kimanin mutane dubu 1,700 zuwa dubu 2,000 ne suke rasa kafar su ko kuma hannun su, a lokacin da ake kokarin kubutar dasu, bayan Micizan sun harbe su.

A jawabinsa na Ranar Wayar da Kai game da Saran Macizai ta bana, Dr Mamora ya ce jihohin da matsalar ta fi kamari a Najeriya su ne Gombe, Filato, Adamawa, Bauchi, Borno, Nasarawa, Enugu, Kogi, Kebbi, Oyo, Binuwai da kuma Taraba.

Mamora ya yi kira a kara kaimi da hadin gwiwa tsakanin jihohin da  matsalar ta fi kamari da kungiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki domin yi wa tufkar hanci.

Shima a jawabinsa, Babban Sakataren Ma’aikatar, Mahmoud Mamman, ya ce mutane dubu 1,793 sun rasu a sakamakon sarar maciji daga 2018 zuwa 2020 inda macizai suka sari mutane dubu 45,834, duk da cewa babu alkaluman wadansu mutanen da macizai suka sara ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: